Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi shelar cewa an kashe zaratan jami’an ta shida, yayin da wasu shida kuma an neme su an rasa, bayan da ‘yan bindiga suka yi masu kwanton-ɓauna a Jihar Delta.
Kakakin Yaɗa Labaran Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, a Abuja, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana haka cikin wata sanarwar da ya buga a shafin tiwita, wato X.
A ranar Asabar ya saki sanarwar, amma bai bayyana ranar da aka kashe ‘yan sandan da kuma ranar da su ma waɗanda aka rasa inda su ke ɗin suka ɓata ba.
Adejobi ya ce ‘yan sandan da kashe da waɗanda ake nema ɗin sun je ne domin binciken yadda wasu abokan aikin su uku suka ɓace a cikin Dajin Ohoro, cikin Jihar Delta.
A can cikin dajin ne ‘yan bindiga suka yi masu kwanton-ɓauna, suka kashe har da insifeto biyu, sajen huɗu, yayin da ake neman insifeto huɗu, sajen biyu har yau shiru, babu labarin su.