‘Yan Bindiga Na Neman Cinye Zamfara Da Ya?i

Rahotanni daga jihar Zamfara na bayyana cewar gamayyar kungiyoyin ‘yan bindiga na kara ?yaimi wajen kai hare-hare a fa?in jihar, da cigaba da tayar da garuruwa da ?auyuwa, duk da sulhu da gwamnan jihar Bello Matawalle ke han?oron yi da ‘yan bindigan.

A halin da ake ciki yanzu ?aruruwan mutanen ‘Yar Nasarawar-Akubu na karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, suna can suna zaman gudun hijira a makwabtan garuruwa, cikin mawuyacin hali da tashin hankali.

Sun fuskanci kalubalen jerin hare-hare har uku da ‘yan bindiga suka kai musu tun daga ranar Talata har zuwa ranar Alhamis babu sassautawa.

Wani mutumin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana wa BBC cewa a halin yanzu babu kowa a garinsu kuma shi ma yana magana ne daga mafakarsa.

“Mutane ne ke taimaka mana da abinci tunda a halin yanzu a gidan wasu muke a zaune. Da mu da matanmu da ‘ya’yanmu, a takure muke, wasu daga cikinmu ma a shago aka dan raba mu muke kwana,”.

A cewarsa, ranar Talata bayan sun idar da sallar la’asar ne ‘yan bindigar suka shiga garinsu tafe a kan babura kusan su 40 suna barin wuta da bindigogi da harbi irin na kan mai uwa da wabi.

“A haka suka kashe mutum 12 sannan wadanda suka tsere ma suka bi su daji suka rika harbinsu.” Ya ce bayan sun gama kashe mutane kuma sun dibi amfanin gona da sauran kayan abinci suka tafi da su.

“Sai da mangariba suka bar garin amma washegari da safiyar ranar Laraba sun sake dawowa a lokacin da muke kokarin yin jana’izar mutanen da suka kashe a daren Talata,” kamar yadda ya shaida.

Ya ce a nan ma sai tserewa mutane suka yi suka bar gawarwakin da ake shirin yi wa sallah. Ya ce maharan ba su kashe kowa ba ranar Laraba amma sun kwashi kayan abinci kuma sun balla shaguna sun yi sata.

Ya ce jami’an tsaro sun isa garin ne da la’asar suka ba mutanen gari kariya har suka yi wa ‘yan uwansu jana’iza. Mutumin ya ce jami’an tsaron ba su tsaya sun ba mutanen garin kariya ba don ana gama jana’izar suka tafi kuma maharan sun sake dawowa ranar Alhamis da safe inda suka tarar da ‘yan tsirarun mutane da suka je tattara sauran amfanin gonarsu.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro musamman ‘yan bindiga masu satar mutane da barayin daji.

Related posts

Leave a Comment