‘Yan Bindiga Na Dab Da Zama Tarihi A Najeriya – Ribadu

images (13)

Mai ba wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya sanar da haka, lokacin da yake ganawa da manema labarai a Jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto.

Ribadu yace gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a shiyar arewa maso yammacin Najeriya, da zaran ta samu labari, kuma wannan na daga cikin nasarorin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu tun daga watan Yunin da ya gabata.

Mai bada shawarar ya tabbatar da matsalolin tsaron da suka addabi kasar da kuma irin illar da suka yiwa jama’a, yayin da yace suna aiki tare da gwamnonin jihohi domin ganin an shawo kan ta da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Ribadu ya bayyana cewar yawan magana kan yi illa ga nasarorin da ake samu, abinda ya sa suka gwammace su ci gaba da aiki ba tare da shelar abinda suke yi ba.

Mai bai wa shugaban shawara yace duk wadanda aka kama da sunan garkuwa da mutane a yankin arewacin Najeriya da gwamnati ta samu labari ya zuwa wannan lokaci ta kubutar da su, kuma gwamnati zata ci gaba da wannan aikin ba tare da kaukautawa ba.

Yace daga cikin wadanda aka kubutar harda dalibai da mazauna kauyukan da aka yi garkuwa da su, domin gwamnati tayi nasarar ganin sun samu yancin kan su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply