‘Yan Arewa Munafukai Ne – Khadijah Ɗiyar Tsohon Sarkin Kano Sunusi

Khadija Sanusi ta wallafa wasu kalamai da suka janyo cece kuce a shafin Twitter inda ta kira yan Arewa da cewar munafukai ne.

Ga dai abunda Gimbiya Khadija tace ‘Yan Arewa munafukai akan addini. Suna ɓuya a bayan “Dokar Shari’a ce” kawai idan dokar tazo daidai da ra’ayin su; idan aka juyo kan maganar – auren mata fiye da daya, ‘yancin mata, da Auren tilas, cin zarafi da sauran su, sai kaga sun makantar da ido sunyi shiru.

Waɗannan kalamai na Gimbiya Khadija, suna zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka mahawara akan matashin da ya yiwa Annabi Muhammadu Batanci.

Labarai Makamanta

Leave a Reply