‘Yan Adawa Ne Ke Zargin An Yi Cushe Cikin Kasafin Kudin 2024 – Tinubu

IMG 20240308 WA0066

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa zargin da ake yi wai an danƙara cushen maƙudan kuɗaɗe cikin kasafin 2024, kawai rashin fahimta ce da masu hauragiya ba su yi wa yadda ake lissafin ƙidayar kasafin kuɗi ba.

Tinubu ya bayyana cewa masu adawa ba su iya bambance aringizo daban, lissafin-dokin-Rano ma daban.

Da ya ke jawabi ranar Alhamis lokacin da ya gayyaci Sanatocin Najeriya yin buɗe-baki a Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya nuna goyon baya ga Sanatocin Najeriya, a inda ya yi magana a karon farko kan zargin maka maƙudan aƙaluman kuɗaɗe a cikin kasafin, lamarin da ya haifar da ka-ce-na-ce.

Tinubu ya ce shi dai ya fahimci asarƙalar da ke tattare da lissafin alƙaluman kasafin kuɗi, wadda sai mai kaifin fahimta ke iya ganewa. Ya ce amma masu adawa idon su ya rufe ba za su iya fahimta ba.

Daga nan ya yi wa Sanatocin addu’a fatan alheri dangane da yadda suka daddale kasafin kuɗi na 2024.

“Ni dai na san yadda lissafin alƙaluman kasafin kuɗi yake. Kuma adadin da na kai Majalisar Dattawa na sani sarai. Na san kuma adadin da aka maido min.

“Saboda haka ina gode maku baki ɗaya saboda yadda kuka bibiyi kasafin tare da daddale shi. Na gode ƙwarai.

“Waɗanda ke surutan wai an kafci maƙudan kuɗaɗe an cusa a cikin kasafin da gangan, ai ba su san bambancin aringizo da lissafin-dokin-Rano a ƙididdiga ba. Kuma ba su koma sun nazarci ainihin adadin da na aika Majalisa ba. Saboda haka ba ku aikata wata harƙalla ko aringizo komai ba,” inji Tinubu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply