Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya zargi gwamnatin tarayya da janye sojojin da ke aiki a wuraren da ke fama da matsalar tsaro a jihar
Yayin da yake amsa tambayoyi a cikin shirin A Faɗa A Cika da BBC Hausa tare da tallafin gidauniyar Mac Athur ke shirya wa, gwamna Lawal ya ce ”muna zaune a wasu lokuta sai a turo daga Abuja a ce a cire waɗannan jami’an tsaro, to ya zan yi”?
Gwamnan ya ce rashin ikon da yake da shi kan jami’an tsaro ne ya sa har yanzu aka kasa magance matsalar tsaron jihar
“‘Ba ni da iko kan ‘yan sanda, ba ni da iko kan sojoji, Wallahi billahi ina mai tabbatar maka cewa idan na ina da iko kan wadannan da yanzu matsalar tsaro a Zamfara ta zama tarihi”, in gwamnan.
Gwamna ya kuma ce duk dokar da ya bai wa jami’an tsaron da ke aiki a jihar, ba su binta, sai abin da aka umarce su daga Abuja.
Ya ce ya gana da shugaban rundunar sojin ƙasa a lokuta da dama a Abuja, sannan sun sha ganawa a Zamfara.
”Na koka masa kan matsalar, kuma suna amsa mana cewa za su yi, amma shiru, a lokacin da ‘yan bindiga suka addabi Tsafe na gana da babban hafsan tsaro na ƙasar, na gana da shugaban ƙasa, na kuma gaya masa matsalar da muke ciki”.
Gwamnan ya ce a lokacin ganawarsa da shugaban ƙasar, ya fahimci cewa akwai abubuwa da dama da aka gaya wa shugaban ƙasar, wanda kuma a zahirin gaskiya ba haka suke ba.
Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalar tsaro, inda ‘yan bindiga ke sace mutane domin neman kuɗin fansa.