Yaki Da Ta’addanci: Najeriya Za Ta Horar Da Sojojin Kasar Chadi

A kokarin Najeriya na ganin bayan ayyukan ta’addanci a faɗin nahiyar Afirka gaba ɗaya, ƙasar ta yi damara wajen bada horo ga sojojin ƙasar Chadi, a matsayin wani mataki na daƙile ayyukan ta’addanci a yankin tafkin Chadi da Sahel.

Babban hafsan sojin ruwa Vice Admiral Awwal Gambo ya bayyana hakan lokacin da jakadan ƙasar Chadi a Najeriya Abakar Chahaimi ya kai ziyara hedikwatar sojin ruwan Najeriya a Abuja.

A cikin wata takardar sanarwar da rundunar sojin ta aika wa manema labarai a ranar Juma’a, ta bayyana cewar Vice Admiral Awwal Gambo ya jinjina wa sojojin Chadi kan rawar da suka taka na tabbatar da tsaro a yankin tafkin Chadi da kuma Sahel.

Shugaban dakarun sojin ruwan ya kuma ce wannan manufa na ɗaya daga cikin manufofin ƙasashen na ƙoƙarin tabbatar da tsaro da kare iyakokinsu daga ayyukan ƴan ta’adda.

‘Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun dade suna addabar kan iyakokin kasashen biyu da hare-haren ta’addanci, ana ganin wannan mataki zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro a yankin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply