Jirgin dakon kaya daga Kasar Rasha ya sauka lafiya a filin jirgin sama na sansanin sojojin saman Nijeriya dake garin Makurdi a jihar Benue.
Jirgin ya sauke wani jirgin yaki na zamani mai saukar ungulu kirar Mi-28NE wanda gwamnatin shugaba Buhari ta saya daga Kasar Rasha domin a yaki ‘yan ta’adda.
Wannan shine jirgin yaki mai saukar ungulu da Nijeriya ta mallaka wanda babu irin sa a kyau da tsada, gudu da kuma gaggawan kaiwa hari
Allah Ya sa su yi amfami da shi yadda ya dace.
Daga Datti Assalafiy