Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Za Ta Yi Ƙarar Malaman Jami’o’i A Kotu

Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta yi barazanar shigar da kungiyar malaman jami’ar Najeriya, ASUU, kara a kotun ma’aikata kan yajin aikin da ta ke yi da ya-ƙi-ci-yaƙi-cinyewa kamar yadda TVC ta ruwaito.

Ministan Kwadago da Ayyuka, Dakta Chris Ngige ne ya yi wannan barazanar a karshen taron da suka yi na tsawon kimanin awa uku da shugbannin kungiyar a Abuja.

Kamar yadda suka saba, bangarorin biyu sun bayyana fatar ganin an kawo karshen yajin aikin a jawabinsu na bude taron.

Amma bayan kimanin awa biyu cikin taron, ASUU ta ce har yanzu babu wani sabon abu da aka gabatar mata.

A hirar da ya yi da manema labarai, Ministan ya ce akwai yiwuwar gwamnati ta dauki matakin shari’a kan malaman jami’ar da ke yajin aiki don kawo karshen rashin jituwar.

A wani labarin daban, kungiyar ta ASUU ta ce kada iyaye su yi tunanin cewa abin da suke nema ya yi yawa da har zai sa su dauki dogon lokaci suna yajin aiki.

An ruwaito cewa kungiyar ta bayyana cewa iyaye su lura cewa idan gwagwarmayarsu ta tashi a banza, “aljihun su zai koka wajen tura yaran su karatu jami’a.”

Shugaban ASUU shiyyar Lagos, Farfesa Olusiji Sowande ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron tattaunawa da kungiyar tayi a jami’ar Olabisi Onabanjo University (OOU), Ago-Iwoye, a jihar Ogun.

Labarai Makamanta

Leave a Reply