Yahudu Da Nasara Ke Daukar Nauyin Masu Bore A Iran – Ayatollah Khamenei

Jagoran addinin Iran ya zargi Amurka da Isra’ila da hannu wurin gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati da ta karade kasar, a jawabin da ya yi kan batun a karon farko.

Ayatollah Ali Khamenei ya ce rikakkun makiya Iran ne suka “kitsa” jerin “bore” da zanga-zangar, yana mai zargin cewa an kona Alkur’anai a wuraren boren.

Ya yi kira ga jami’an tsaro su yi damarar fuskantar karin zanga-zangar da za a yi.

Zanga-zangar – wadda ta kasance kalubale mafi girma na mulkin da ya kwashe tsawon shekaru yana yi – ta faru ne bayan mutuwar wata matashiya a hannun ‘yan Hisbah.

Mahsa Amini, mai shekara 22, ta fada halin rai kwakwai mutu kwakwai bayan ‘yan Hisbah sun kama ta ranar 13 ga watan Satumba a Tehran bisa zargin keta dokar sanya hijabi ko kallabi. Ta mutu kwana uku bayan haka.

Iyayenta sun yi zargin cewa ‘yan Hisbah sun doke ta da kulki a ka sannan suka gwara kanta da jikin motarsu. ‘Yan Hisbar sun ce babu wata shaida da ta nuna cewa sun aikata laifin da ake zarginsu da shi suna masu cewa ta yi fama da “bugun zuciya na farat daya”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply