Yayin da jam’iyyu ke shirin tunkarar zaben gwamna dana ‘yan majalisun dokokin jihohi a Najeriya, wani batu da ke fitowa fili a fagen siyasar jihar Kaduna shi ne na siyasar addini da kuma ?abilanci.
A baya dai jihar ta sha fama da rikice-rikice masu nasaba da addini da kabilanci, lamarin da masana ke nan suka ce yana matukar janyo komawa baya ga tsarin dimmkradiyya.
Duk da cewa akwai masu neman takarar kujerar gwamna a jihar fiye da 10, takarar tafi zafi ne a tsakanin jam’iyyar APC da kuma PDP.
Masana harkokin siyasa a jihar dai sun fara nuna damuwa a kan yadda salon siyasar jihar ya dauka inda batun addini da kuma bangaranci ke jujjuya alkibilar siyasa a baya bayan nan a jihar.
Dakta Haruna Yakubu Ja’i, masanin siyasa ne a jami’ar jihar Kaduna, ya shaida wa BBC cewa idan aka lura yanzu malaman addinai da kuma shugabannin majami’u sun dukufa wajen nunawa mabiyansu cewa ga wanda zasu zaba saboda shi ne zai wakilci addininsu ko kuma yankinsu.
Ya ce, ‘’ A gaskiya a tsari na siyasa ba wannan ake dubawa ba,”
Masanin ya ce muddin za a yi amfani da addini ko kabilanci a tsarin siyasa to za a iya fuskantar babbar illa a tsarin dimokradiyyar jiha koma kasa.
Ya ce, ‘’ Bin irin wannan tsari ya kan sa a hana wa mutane zabar wanda suke gani zai iya yi musu jagoranci da kuma kawo musu shugabanci na gari saboda an saka addini a ciki.”
Dakta Haruna Yakubu Ja’i, ya ce haka suma shugabannin addinin idan suka sanya mutane suka zabi wadanda basu dace ba, wanda daga baya ba a samu abin da ake so ba daga wajensu, sai suzo suna jin kunyar mutane, saboda sun sa su zabar tumin dare.
Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin Najeriyar da hankula zasu karkata musamman ganin irin yadda fagen siyasar jihar ke kara daukar dumi.