Yadda Na Ku?uta Daga Hannun ‘Yan Bindiga – Mai Shunku

Fittacen jarumin Kannywood Ibrahim Mai Shunku ya bayyana wata gagarumar jarabawar da ta same su da abokanan shi.

“Ranar Talata goma ga watan Nuwamba shekarar dubu biyu da Ashirin (10/09/2020) muka hadu wata gagarumar jarabawar da banyi niyar bayyana ta a shafukan sada zumunta ba amma ya zama dole saboda muna bukatar addu’ar ku .

kan hanyar mu ta zuwa kaduna daga Abuja. Muka yi arba da masu garkuwa da mutane inda saka bude wa motocin mu wuta na kusan mintuna talatin ba sassautawa. wannan dalilin ya yi sanadiyyar rasa rayukun sama da mutane goma suka kuma yi awon gaba da kusan mutane sama da shabiyar a cikin tawagar tamu da kuma wasu mutane daban.

Cikin mutanen da a kayi a won gaba da su akwai hadimin shubagan kasar Najeriya Alh Abdullahi Abubakar Wali shugaban Kungiyar Nigerian youth organization (NYO) da sauran mutane da yawa. Muna bukatar addu’ar ku akan Allah ya kubutar da su ” kamar yanda jarumin ya bayyana a shafinsa na Instagram

DAGA Abdoulfatah Omar

Related posts

Leave a Comment