A ranar asabar din da ta gabata ne, ‘Yan bindiga dauke da makamai, sun kai hari a kauyen Biya-Ki -Kwana da ke cikin karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, inda suka sace Suwaiba Naziru tare da danta dan shekara biyu da rabi, da wasu Mata goma.
Da take ba da labarin yadda aka sace su, ta fara da cewa da misalin karfe takwas ne na daren ranar asabar, na je yin wayar da Maigidana, domin sanar da shi halin rashin kudin tafiyar da rayuwa, wato abinci, da yake ya na neman kudi a kudanci Nijeriya. Akan hanyar dawo wa gida na hadu da su, sun dauko wasu Mata yan garinmu, suka ce mu tafi, na ce ina dauke da tsohan ciki, suka ce ba su yadda ba, suka tilasta man bin su, mu ka cigaba da tafiya a kasa kamar garken tumaki.
Sawaiba ‘yar shekara ashirin da biyu ce, ta kara da cewa muka ci gaba da tafiya, mun ci tafiyar kilomita da yawa har muka je wani garin Rinji, inda anan ne suka dora mu bisa mashina, har zuwa cikin daji Maboyar su. Ga shi ina goye da yaro na, dan shekara ukku a bayana, na sha wahala sosai wadda ba ta misaltuwa, ga tsohan ciki ga goyo ga tafiyar kasa mai nisa kuma cikin dare har gari ya waye.
Malama Suwaiba Naziru ta ci gaba da cewa da na fara nakuda, sai daya daga cikin wadanda aka sato mu tare, ta zama unguwar zoma, wadanda suka sace mu suka ba ta rezar da ta yankewa jaririn cibi. Yan bindiga suka kawo mana ruwan zafi na yi wanka na wanke jaririn, daga nan suka ce za su je su sanar da ogansu, domin su samu umurnin sa a salla me ni, in tafi gida, bayan tsawon lokaci ba su dawo ba, can bayan tsawon lokaci sai ga su, suka dauko ni da yarana biyu bisa babur har zuwa kauyen ‘Yangeza daga nan sai muka hau wani mashin sai gida.