Yada Labaran Karya: NBC Ta Ci Tarar Gidan Talabijin Na Arise

Hukumar kula da kafafen yaɗa labaru ta ƙasa NBC ta ci tarar kafar yaɗa labaru ta Arise saboda zargin ta da yaɗa labarin ƙarya.

A ƙarshen makon da ya gabata ne Arise TV ya yi wani labari da ke cewa hukumar zaɓe na binciken ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Tinubu, bisa dogaro da wani labarin da aka rinƙa yaɗawa a shafukan intanet.

NBC ta ce abin da kafar Arise ta yi, “gagarumin karan-tsaye ne ga dokar yaɗa labaru ta ƙasa sashe na 5.1.3, da rashin iya aiki, da kuma rashin tunani a wannan lokaci da ake yaƙin neman zaɓe.”

Saboda haka sanarwar wadda ta samu sa hannun shugaban hukumar, Balarabe Shehu Illela, ta buƙaci Arise TV ya biya tarar naira miliyan biyu a cikin wa’adin mako biyu.

A ranar Lahadi ne dai kafar Talabijin ɗin na Arise ya nemi afuwar ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar A.P.C, bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta fitar da wani bayani kan cewar labarin da ake yaɗawa da ke cewa tana bincike kan Bola Tinibu ba gaskiya ba ne.

Hukumar ta NBC ta kuma buƙaci kakafen yaɗa labaru da su rinƙa tantance duk wani labari da suka samu gabanin wallafa shi, musamman ma wanda aka samu a shafukan sada zumunta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply