Ya Zama Dole Mu Hada Hannu Wurin Ceto Najeriya – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar kuma ?an takarar Shugabancin ?asa ?ar?ashin jam’iyyar PDP a zaben 2019 da ya gabata, ya ce halin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki yanzu ba abu ne da za a zura ido kawai ana kallo ba, ya zama wajibi a tashi tsaye a taimakawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari domin fidda A’i daga rogo.

Wazirin na Adamawa Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a cikin wata makala da ya gabatar mai taken: ‘Matsakaicin rashin aikin yi mafi girma a Duniya: Lokaci Don Taimakawa Wannan Gwamnati ta Taimakawa Najeriya’.

Tsohon mataimakin shugaban kasar bayyana cewa, taimakawa wannan gwamnati mai ci shine mataki na ceton ilahirin ‘yan Najeriya daga afkawa cikin matsalar dake fuskantar su.

Ya ce abin takaici ne maimakon sauraran shawarwari, sai ya zamana gwamnatin tana karantar ma’anoni marasa kyau ga ra’ayoyi da shawarwarin da masu sukarta ke bayarwa.

Atiku ya kuma danganta yawaitar aikata laifuka da rashin aikin yi da kasar ke fuskanta wanda ba a taba gani ba. “Ban taba jin bakin ciki sosai ba, kamar yadda naji yayin da naga rahoto daga Bloomberg Business a ranar Asabar, 27 ga Maris, 2021 cewa Najeriya za ta fito a matsayin kasar da ke kan gaba wajen yawan marasa aikin yi a duniya, a kan sama da 33%.

“Mun yi gargadi game da wannan, amma fadakarwar da ni da wasu masu kishin kasa suka yi a banza, gashi yanzu an zo wajen kowa yana ji a jikinshi.

Related posts

Leave a Comment