Kungiyar cigaban siyasa da zamantakewar Yarabawa, Afenifere, ta shaida wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu cewa ba shi da wani uzuri na kin sake fasalin Najeriya kasancewar an zabe shi a kan dandamali da akidar kungiyar.
Afenifere ta kuma bayyana cewa kundin tsarin ta na sake fasalin Najeriya nan ta tanade shi.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ?ungiyar ta ce ?ora kundin sake fasalin Nijeriya ne akan doron tsarin mulkin firaminista a ?asar.
Sakataren yada labarai na Afenifere, Mogaji Gboyega Adejumo, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron shugabannin kungiyar da aka gudanar a Isanya Ogbo Ijebu dake jihar Ogun a gidan Pa Ayo Adebajo, shugaban kungiyar Afenifere.
Kungiyar Afenifere, wacce ke daya daga cikin masu fafutukar kawo sauyi a Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai tattara ra’ayoyin masu ruwa da tsaki kan wannan bukata.
A taron kungiyar ta Afenifere da aka gudanar a yau Talata, kwamitin ya mika rahotonsa.
Adejumo ya ce kungiyar Afenifere ta bullo da tsarin sake fasalin kasar nan inda ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta yi amfani da tsarin.
Kungiyar ta ce Tinubu, kafin zaben sa yana kan gaba wajen kiran a sake fasalin kasar nan, don haka bai kamata ya ci amanar ‘yan Najeriya ba.
Afenifere ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya ci gajiyar kiran a sake fasalin tsarin mulkin dimokuradiyya, don haka ba shi da hujjar da zai ?i sake fasalin ?asar.