Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sanata Ali Ndume, sanata mai wakiltar Borno ta kudu, yace mayakan Boko Haram da suka mika wuya, “Wa?anda akwai sauran burbushin ta’addanci a zukatansu, kamata yayi a binciko su, a hukunta su.”
Da yake jawabi a Abuja, jim ka?an bayan ganawa da shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, sanatan ya jaddada cewa bai kamata a saki jiki da tubabbun lokaci guda ba, domin yin hakan akwai hatsari.
Sanatan yace ya kamata gwamnati ta bi dokar ?asa da kuma ta kasa-da-kasa wajen amsar tubabbun yan ta’addan, domin kaucewa shiga ru?ani.
“Har yanzun ina nan akan magana ta kan yan ta’addan dake mika wuya, wasu ne kawai suke fassara zance na ta yadda ransu yake so.” “Akwai dokar ?asa da ta yi bayani kan irin haka, hakazalika akwai dokokin kasa-da-kasa da suka yi bayani kan irin haka saboda wannan ba shine karo na farko da aka samu irin wannan ?alubalen a kasashen duniya ba.”
“Duk lokacin da ka fita fagen yaki, kodai ka ci nasara ko abokin fa?anka ya mika wuya, idan ya mika wuya ka rasa damar hukunta shi amma ba zaka ce ba shi da laifi ba.”
“A amince musu, a ?auki bayanansu, sannan a bincike su, wa?anda suka mika wuya dagaske a kyale su, amma duk wandanda akwai ?ur?ushin tunanin ta’addanci a zuciyarsu, a gurfanar da su.” “Idan mutum ya mika wuya a ba shi dama, matukar ka tuba to baza’a hukunta ka kai tsaye ba, za’a baka dama kaje kotu ka tabbatar da tubarka ko akasin haka, wannan shi nake bukata gwamnati ta yi.”