Ya Kamata Najeriya Ta Koma Salon Mulkin Shugaban Kasa Na Jeka Nayi Ka – Na’ Abba

An bayyana cewar salon tsarin mulki da Najeriya ke kai a halin yanzu na Shugaban ?asa mai cikakken iko ko ka?an bai dace da tsari na ?asar Najeriya ba, domin ya bada wata dama ce ga shugaban kasa na yin mulkin danniya, wanda hakan ya taimaka gaya wajen jefa kasar halin da take ciki na koma baya a yanzu.

Tsohon Shugaban majalisar wakilai na Tarayya Alhaji Ghali Umar Na’ Abba ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da shi a cikin shiri na musamman mai suna “State Of Union” na Gidan talabijin na Liberty dake birnin tarayya Abuja.

Ghali Na’ Abba ya ?ara da cewar muddin ya zamana Najeriya ta ?auki salon tsarin mulkin Shugaban ?asa na jeka nayi ka, hakan zai taimakawa ‘yan ?asar da sauran za?a??u wajen sauke nauyin dake kansu.

Tsohon Shugaban majalisar ya koka tare da sukar lamirin Shugabancin Shugaban ?asa Buhari, wanda ya bayyana shi mafi muni a tarihin shugabancin kasa a Najeriya.
“Komai ya durkushe a wannan mulkin, babu wani abu guda dake tafiya bisa tsari, harkar tattalin arziki ta sunkuya, sha’anin tsaro ya ta?ar?are ga masifar tsadar rayuwa a tsakanin jama’a”.

Ghali Na’ Abba yace salon siyasar Najeriya na fuskantar koma baya tun bayan da kasar ta koma bin tafarkin dimukura?iyya a shekarar 1999, sannan al’amarin ya ?ara ta?ar?arewa a wannan lokaci sakamakon yadda gwamnati mai ci tayi watsi da nauyin da ke kafa?unta, ba ta saurarer shawarar masana.

Dangane da cece kucen da ake ciki na batun yin sulhu da ‘yan bindaga kuwa, tsohon shugaban majalisar ya goyi bayan matakin yin sulhun, inda yace galibin matsalolin da ake fuskanta za’a iya shawo kansu idan aka bi tsari na zama a teburin shawara fiye da ?aukar zafi.

Ghali Na’Abba ya kuma nuna damuwa da takaici dangane da kalaman da ministan tsaro Bashir Magashi ya yi kwanan nan na cewar ‘yan Najeriya su kare kansu daga ‘yan bindaga, inda yace wannan kalami ba ?aramin kuskure ba ne, kuma nuna gazawar Gwamnati ne sannan zai sanya jama’a su samu fargaba da rashin tabbas a ?angaren gwamnati.

Tsohon Shugaban majalisar ya kuma nuna damuwar shi dangane da yadda wasu jama’a ?alilan ne ke sarrafa abin da ya dace Miliyoyin jama’a su amfana da shi, inda ya bada misali akan yadda Gwamnoni suka jefa jam’iyyu cikin aljifansu sai yadda suka ga dama.

Related posts

Leave a Comment