Ya Kamata Najeriya Ta Koma Salon Mulkin Shugaban Kasa Na Jeka Nayi Ka – Na’ Abba

An bayyana cewar salon tsarin mulki da Najeriya ke kai a halin yanzu na Shugaban ƙasa mai cikakken iko ko kaɗan bai dace da tsari na ƙasar Najeriya ba, domin ya bada wata dama ce ga shugaban kasa na yin mulkin danniya, wanda hakan ya taimaka gaya wajen jefa kasar halin da take ciki na koma baya a yanzu.

Tsohon Shugaban majalisar wakilai na Tarayya Alhaji Ghali Umar Na’ Abba ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da shi a cikin shiri na musamman mai suna “State Of Union” na Gidan talabijin na Liberty dake birnin tarayya Abuja.

Ghali Na’ Abba ya ƙara da cewar muddin ya zamana Najeriya ta ɗauki salon tsarin mulkin Shugaban ƙasa na jeka nayi ka, hakan zai taimakawa ‘yan ƙasar da sauran zaɓaɓɓu wajen sauke nauyin dake kansu.

Tsohon Shugaban majalisar ya koka tare da sukar lamirin Shugabancin Shugaban ƙasa Buhari, wanda ya bayyana shi mafi muni a tarihin shugabancin kasa a Najeriya.
“Komai ya durkushe a wannan mulkin, babu wani abu guda dake tafiya bisa tsari, harkar tattalin arziki ta sunkuya, sha’anin tsaro ya taɓarɓare ga masifar tsadar rayuwa a tsakanin jama’a”.

Ghali Na’ Abba yace salon siyasar Najeriya na fuskantar koma baya tun bayan da kasar ta koma bin tafarkin dimukuraɗiyya a shekarar 1999, sannan al’amarin ya ƙara taɓarɓarewa a wannan lokaci sakamakon yadda gwamnati mai ci tayi watsi da nauyin da ke kafaɗunta, ba ta saurarer shawarar masana.

Dangane da cece kucen da ake ciki na batun yin sulhu da ‘yan bindaga kuwa, tsohon shugaban majalisar ya goyi bayan matakin yin sulhun, inda yace galibin matsalolin da ake fuskanta za’a iya shawo kansu idan aka bi tsari na zama a teburin shawara fiye da ɗaukar zafi.

Ghali Na’Abba ya kuma nuna damuwa da takaici dangane da kalaman da ministan tsaro Bashir Magashi ya yi kwanan nan na cewar ‘yan Najeriya su kare kansu daga ‘yan bindaga, inda yace wannan kalami ba ƙaramin kuskure ba ne, kuma nuna gazawar Gwamnati ne sannan zai sanya jama’a su samu fargaba da rashin tabbas a ɓangaren gwamnati.

Tsohon Shugaban majalisar ya kuma nuna damuwar shi dangane da yadda wasu jama’a ƙalilan ne ke sarrafa abin da ya dace Miliyoyin jama’a su amfana da shi, inda ya bada misali akan yadda Gwamnoni suka jefa jam’iyyu cikin aljifansu sai yadda suka ga dama.

Labarai Makamanta

Leave a Reply