Ƙungiyar tuntuba ta magabatan Arewa (ACF) a ta yi gargaɗin cewa ya kamata shugabanni a Najeriya su sani cewa, a wani lokaci ne na saurarar buƙatun jama’a, saboda bai dace ba a cigaba da yin biris da matasa da kuma buƙatunsu ba.
Dattawan Arewa sun bayyana cewa cigaba da yin ko ina kula da bukatun matasa tare da matsalolinsu kan iya janyo gagarumar matsala a kasa, wadda ba’a san iyakar ƙarshen ta ba.
Shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa na ACF, Audu Ogbeh, ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa na manyan shugabannin al-umma na ƙasa da aka yi a garin Kaduna tarayyar Najeriya.
“Halin da ake ciki na zullumi da fargaba musamman a arewacin ƙasar nan babbar barazana ce ga zaman lafiya da cigaban yankin da kuma ƙasa baki ɗaya,” a cewar Ogbeh.
Kalaman na Ogbeh sun zo ne a kan gaɓar hargitsi da ake fama dashi a wasu jihohi a ƙasar nan bayan matasa sun shafe kusan mako biyu suna gudanar da zanga-zanga don ganin sun kawo ƙarshen zaluncin ƴansanda.
Dattijo Audu Ogbeh ya ce a halin da ake ciki, akwai buƙatar shugabanni su sauya salo da dabaru, sannan su maida hankali a kan cigaban kasa musamman inda muke fuskantar ƙalubale da suka shafi ɓangarorin siyasa, tattalin arziƙi da kuma zamantakewa.
“Za mu iya, kuma dole mu fuskanci abin da yake gabanmu ta hanyar zuba hannun jari a harkar ilmi, noma da kiwo da kuma masana’antu. “Dole ne mu tafi da matasa, wadanda dama ƴaƴanmu ne, sannan mu haɗa hannu da su, mu tallafa musu, har ma mu koya daga gare su.
Lokaci ya wuce da zamu yi watsi dasu da buƙatunsu. Yin biris da matasa tamkar mun daɓawa kan mu wuƙa ne,” a cewarsa. Shugaban na ACF ya ƙara da cewa; “halin zullumi da fargaba na matasa musamman a arewacin Najeriya babbar barazana ce ga yankin da kuma ƙasa baki ɗaya.”
“Ina sa ran cewa yanzu, fiye da lokutan baya, shine lokacin da masu ruwa da tsaki za su saka hannu don a magance matsalolin kasa da kuma ceto makomar yaranmu.”