Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Ya Kamata A Rataye Masu Aikata Fyade – Jaruma Fati Muhammad

A tattaunawar da sashin Hausa na gidan Rediyon BBC ya yi da ita, tsohuwar jarumar Finafinan Hausa Fati Muhammad ta bayyana cewar tana goyon bayan zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga dukkanin wanda aka kama da aikata fyade a Najeriya.

Fati Muhammad ta ƙara da cewar aikata fyade mummunan zunubi ne da kassara rayuwar matan da aka aikata mawa, yana kama da kisan kai ne, domin duk wadda aka yi wa fyade to tamkar an kashe ta ne, bisa ga haka tana goyon bayan a kashe duk wanda aka kama da laifin aikata fyade.

Tsohuwar jarumar ta bayyana cewar an daina ganin ta a Finafinan ne saboda shiga harkokin kasuwanci da siyasa da ta yi da kuma bayar da dama ga ‘yan baya suma su gwada tasu bajintar.

“Babban abin da ya ja hankalina ga siyasa shine tsarin gudanar da siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ta dalilin shi na shiga siyasa kuma shine ubangidana a harkar siyasa”.

Dangane da batun aure kuwa tsohuwar Jarumar tace tana nan ta dukufa yin addu’a domin dacewa da mutumin kirki, domin babban burin rayuwarta shine ta yi aure ta samu ‘ya’ya.

Exit mobile version