Yaƙin Neman Zabe: Gwamnatin Adamawa Ta Hana APC Filin Taro

Rahoton dake shigo mana daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar Gwamnatin jihar karkashin jagorancin mai girma Rt Hon Ahmadu Fintiri ta hana yin taron jam,iyyar APC a babban filin Taro na Ribadu Square da ke Jimeta wanda yar takara Gwamnan APC Aishatu Dahiru Binani zata kaddamar da yakin neman zaben ta ranar litinin 9 ga wannan watan.

Sai dai Gwamnatin Adamawa ta fadi dalilai da yasa suka hana gudanar da taron jam,iyyar ta bakin sakatarensa cewa za’a gyara filin ne shine musababbin hana taro a wurin inji Kumanger

Hakan kuma jam,iyyar APC ta ce tuni ta samu sabon filin taro na Baba Zango daura da shatetale mai Dauki, ana kuma saran shugaban kasa Muhammadu Buhari shima zai halarci gangamin

Labarai Makamanta

Leave a Reply