Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda: Rashin Kuɗi Na Kawo Mana Cikas – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya daura laifin rashin samun nasarar yakin yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso gabashin Nijeriya kan rashin isasshen kudi a baitul malin gwamnati.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ganawar su da kungiyar gwamnonin yankin Arewa maso yamma a fadarsa dake Aso Villa.

Ya kara da cewa cutar corona ce ta kara tsananta lamarin.

Amma ya ce akwai damuwa matuka bisa yadda matsalar tsaro ke tsananta fiye da yadda ya samu abin lokacin da ya dau ragamar mulki.

Muna da matsalan rashin kudi da rashin tsaro. Kun san gado mukayi. Amma ya kamata Al’ummar Arewa maso yamma su godewa abinda gwamnatin nan tayi.” Buhari yace

Rahoton da nike samu, da kuma labaran leken asiri shine hukumar Soji ta sake zanga dantse kuma wannan shine gaskiyan lamari.

Na kan samu labaran akai-akai kuma ya zama wajibi in yarda yanzu. Na saurari jawabanku, gwamnan dake samun matsala yanzu a Arewa maso gabas, Adamawa, Bauchi da sauransu na jin dadin zaman lafiya yanzu. Ina kyautata zaton suna godiya bisa sadaukarwan da Soji sukayi.

Ina tabbatar muku da cewa gwamnati na iyakan kokarinta. Rashin kudi ya zame mana kalubale.

Labarai Makamanta

Leave a Reply