Gwamnatin tarayya ta hannun Ma’aikatar agaji da jin ƙai ta fara raba wa matan karkara kudi Naira dubu 20-20 a karkashin shirin bayar da tallafi ga matan karkara 4,000 a jihar Kaduna domin rage talauci.
A cewar gwamnatin tarayya, za a zabi matan 4,000 a fadin kananan hukumomi 23 na jihar waɗanda aka tabbatar suna fama da matsanancin talauci.
An gabatar da shirin a cikin shekarar 2020 don ci gaba da aiwatar da tsarin zamantakewa a Gwamnatin Shugaba Buhari.
Babban Sakataren Ma’aikatar Bashir Nura Alkali, ya wakilci Ministar jin kai da Harkokin Ci Gaban Jama’a Hajiya Sadiya Umar Faruq a taron bude shirin da aka gudanar a Jihar Kaduna.
Ya bayyana cewa “ya yi daidai da hangen nesa ga ‘yan kasa na Shugaba Muhammad Buhari na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru 10.
Ya ce an tsara shirin ne don samar da tallafi sau daya ga wasu mata masu karamin karfi da masu rauni a yankunan karkara da birane na kasar.
“Za a raba tallafin kudi na N20,000.00 ga mata masu karamin karfi kimanin 125,000 a fadin Jihohi 36 na Tarayya da Babban Birnin Tarayya.
“Burinmu a Jihar Kaduna shi ne bayar da tallafin ga sama da mutane 4,000 a fadin kananan hukumomin 23.” inji shi.
A nata jawabin, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe ta ce “COVID-19 har yanzu yana yin mummunan tasiri a rayuwar mutane musamman mata.
Ta ce bayar da kudin babu shakka zai kawo taimako ga mata a cikin al’umma, musamman wajen karfafa kudaden shigansu.