Ya?i Da Ta’addanci: Sojojin Najeriya Ne Kan Gaba A Afirka – Magashi

Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi, ya ce sojojin Najeriya suna daga cikin sojoji mafi nagarta a Afirka, wa?anda suke taka rawar gani wajen da?ile ayyukan ‘yan ta’adda da Ta’addanci a fadin Nahiyar.

Minista Magashi ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, inda yace suna da damar kawo karshen duk wani makiyi idan aka ba su damar yin hakan. A cewar Magashi, rundunar soji za ta iya kawo karshen Boko Haram a arewa maso gabas, saboda sun ci nasara a yakin da suka je cikin wasu kasashen ketare.

A cewarsa, “A Afirka, ya kamata sojojin Najeriya su zama na daya a kwazo, saboda mun dade muna samun nasarori har a kasashen ketare. Mun je ECOMOG, mun yi iyakar kokarinmu. Mun je Sierra Leone, mun ci nasara. Amma sakamakon dadewar wannan yakin, mutane har sun gaji.

“Yan Boko Haram ba sa tsayawa wuri daya, da zarar sun kai farmaki wani wuri sai su gudu su koma wani wurin. Matsalar kawai ba mu san inda suke zama bane.
Yanzu kuwa da muka gano su, gashi nan rundunar sojin sama da ta kasa suna karar da su.”

Related posts

Leave a Comment