Yaƙi Da Ta’addanci: Sojin Sama Sun Tarwatsa Sansanin Boko Haram

Sojojin Saman Nijeriya dake karkashin Rundunar Operation Lafiya Dole, sun yi daga-daga da Boko Haram din da ke cikin sansanin ta’addanci na Tafkin Chadi.

Wadanda aka karkashen an tabbatar da cewa duk wadanda ke bangaren ISWAP ne, kamar yadda jami’in yada labarai na Ma’aikatar Tsaro, John Enenche ya bayyana cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Enenche ya ce farmakin da aka Kai wa yan ta’adda ta jiragen yaki, na daga cikin gagarimin shirin kakkabe ta’addanci baki daya da ake yi a Arewa maso Gabas baki daya.

Ya ce an yi wa Boko Haram ruwan wuta ta saman jiragen yaki ne a ranar 12 Ga Agusta, bayan an samu rahotannin sirri na dandazon wasu masu ta’addanci a wani kauyen da suka ci da yaki.

Ya ce nan da nan Rundunar Sojojin Sama ta tura wasu zarata a cikin jiragen yaki suka kai gagarimin hari a waccan mabuyar da suka yi, bayan an tabbatar da daidai inda suka yi dandazo.

Na’urar da sojojin sama suka yi amfani da ita wajen gano daidai inda Boko Haram (ISWAP) suka yi dandazo, ta nuno su kuru-kuru a wurin.

Daga nan ne fa aka gaggauta tura jiragen yaki suka rika sakar musu wuta tare da kone sansanin. An kuma kashe Boko Haram din da dama a yayin kai farmakin.

Babban Hafsan Sojojin Saman Najeriya, Sadique Abubakar ya jinjina wa Sojojin saboda jimirin su da jajircewa wajen nuna tsananin kishin kasa da kuma kwarewa.

Daga nan sai ya kara zaburar da su kan ci gaba da kai wa Boko Haram hari har a murkushe su gaba daya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply