Yaƙi Da Rashawa: Ka Kori Malami In Har Da Gaske Ne – Lauya Ga Buhari

Kabir Akingbolu, lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kori Abubakar Malami, Antoni janar na tarayya kuma ministan shari’a.

Da yake zargin Malami da amfani da kujerarsa ba ta yadda ya dace ba, lauyan ya shawarci shugaban kasa da ya dauki mataki in har da gaske yana yaki da rashawa.

Jaridar The Cable ta ruwaito yadda Malami ya saka lauyoyin Najeriya biyu Oladipo Okpeseyi da Temitope Adebayo, don samo kudin Abacha har $321 miliyan daga Switzerland, aikin da Enrico Monfrini, wani lauyan kasar ya rigada ya yi tun 2000.

A wata wasika ga shugaban kasa, Akingbolu ya ce AGF Malami ya yi kunnen uwar-shegu a kan kasancewar Monfrini a dawo da kudin duk da kokawar da aka yi kan lamarin.

“A 2018, duk da cewar lauyoyi da dama sun yi aiki tare da kammala dukkanin tsarin dawo da kudin Abachan, sai da Malami ya tabbatar da ya cire wa kansa dala miliyan 16.4 kaso 10 bisa 100 ta hannun abokansa,” in ji shi.

“Kowa a Najeriya ya koka da yadda lauyan ya yi aikin amma Malami ya yi burus tare da karbar kudin. A 2019, Malami ya janye zargin wawurar dala biliyan 25 na cikin kudin da aka samo daga Sanata Danjuma Goje ba tare da wani bayani ba.

“A watan Yunin 2020, Malami ya janye zargin ta’addanci da ake wa wasu sojoji tare da Wadume, kwararren mai garkuwa da mutane kuma dan fashi.

“Ya cigaba da bai wa gwamnatin tarayya shawarwari marasa kyau tare da sanya su take dokar kotu wanda hakan yasa aka tsare Omoyele Sowore, El Zakzaky, Sambo Dasuki da sauran wadanda kotu ta bada umarnin sakinsu.

“Akwai zargin Malami ya mallaki wasu dukiyoyin da suka hada da: Otal na Rayhaan wanda darajarsa ya kai miliyan 500 wanda ke kallon asibitin Malam Aminu Kano da ke kan titin Zaria a jihar Kano.

“Wannan gwamnatin bata da hujja idan ta ki dakatar da Malami ko kuma korarsa idan ya ki bayanin yadda ya siyar da man fetur bayan ya kwace shi.

“Idan gwamnati ta ci gaba da yin shiru tare da fifita Malami, gwamnatin ta manta da wani yaki da rashawa da tace tana yi tare da daina yaudarar ‘yan Najeriya da duniya baki daya.”

Lauyan ya kuma bayyana cewa akwai yuwuwar ya rubuta korafi da zai sa IGP Mohammed Adamu ya yi abinda ya dace idan gwamnati ta ki bincikar Malami.

Tun farko, Akingbolu ya ce akwai yuwuwar Malami ya kwashe shekaru biyar a gidan yari a kan amincewa da yayi aka yi gwanjan man fetur.

Labarai Makamanta

Leave a Reply