Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr. Isa Ali Pantami ya ce akwai bukatar shigar da hukunce-hukuncen addini cikin dokokin yaki da fyaɗe, tun da a cewarsa addini ya yi magana a kansu.
Idan fyade babu amfani da ƙarfi, babu barazana ga ran mace ko ga mutuncinta, to ana ɗaukar wannan al’amari a matsayin zina ne kamar yadda ya zo cikin suratul Annur,” in ji Pantami.
Sai dai ya ce matuƙar an yi amfani da ƙarfi da barazana kamar ta makami, to wannan hukuncinsa na cikin suratul Ma’idah.
Dr. Pantami ya kuma ce waɗannan dokoki ne na Allah, kuma al’ummomin da suka kwatanta aiki da su, sun zauna lafiya.
Shi ma Sheikh Ibrahim Daurawa fitacen malamin addini ne da ke cewa fyade mumunan laifi ne a addinin Musulunci kuma ana iya yi wa mace ko namji.
Hukunce-hukuncen fyade sun kasu kashi 4 kamar yadda ya zo a cikin kundin yanke hukunci wanda malamai suka ba da fatawarsa a kasar Saudiya, in ji Daurawa.
Idan ya zama wanda aka yi wa fyaden mace ce babba ko karama sannan wanda aka yiwa fyaden na da aure ko babu aure, sannan namiji ne ko mace akwai abubuwan da ake duba wa.
Haka kuma Idan mutum namiji ya yi wa mace fyade ana duba a ina ya yi mata fyaden, gidansa taje ko kuma shine yaje gidanta, sannan a wurin aiki ne ko kan hanya, sai a lura da yanayin da abin ya faru.