Ministan Lafiya, Osagie Ehinare ya bayyana cewa ma’aikatar sa za ta rabawa jihohin kasar nan 36 da Abuja tallafin naira miliyan 100-100 domin cigaba da ayyukan dakile yaduwar corona a jihohinsu.
Ehinare ya ce wannan kudi daga cikin kudin wani shirin Bankin duniya ne domin kasashen kasashen Afrika Ta Yamma, tallafin annobar Ebola.
Bayan haka shugaban kwamitin shugaban Kasa, kan dakile yaduwar Korona, ya bayyana cewa kasar Indiya ta baiwa Najeriya gudunmawar maganin Chloroquine domin kula da marasa lafiya.
Akarshe ya yi kira ga mutane su ci gaba da bin dokokin Korona.