Yaƙi Da CORONA: Ganduje Abin Koyi Ne – NCDC

Hukumar Kiyaye Cututtuka Masu Yaɗuwa, NCDC, ta yabawa jihar Kano saboda zama zakara wurin gwajin korona a ƙasa baki ɗaya.

“Kano tana yi gwaji fiye da ko wane jiha a Nijeriya,” a cewar shugaban NCDC, Dr Choker Ihekweazu.

Shugaban na NCDC na ƙasa ya yabawa Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje saboda jajircewarsa wurin yaƙi da annobar ta Covid-19.

Sanarwar ta babban sakataren watsa labarai na gwamnan Abba Anwar ta ce Shugaban na NCDC ya bukaci sauran jihohi suyi koyi da jihar ta Kano.

Ihekweazu ya lura cewa a halin yanzu ba a samun yaduwar cutar kamar yadda ake samu a baya kuma ya gamsu da halin da jihar ke ciki a yanzu.

An gano cewa gwamnatin jihar Kano ta yi farin ciki da wannan yabon da NCDC ta yi mata.

“Wannan jinjinar za ta ƙara wa gwamnan da al’ummar jihar ƙwarin gwiwa su ƙara jajircewa wurin yaƙi da coronavirus,” kamar yadda wani jami’in gwamnati ya shaidawa The Nation.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa Akin Abayomi, kwamishinan lafiya na jihar Legas, ya ce gwamnati na kashe kimanin N500,000 zuwa Naira miliyan 1 kan kowanne mai cutar korona a jihar idan ta tsananta.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, Abayomi ya ce yawan kudin da ake kashewa majinyatan cutar ya danganta ne da tsananin da cutar ta yi.

Kwamishinan ya ce suna kashe kusan N100,000 ga majinyacin cutar da bata yi wa tsananin kamu ba.

“Domin maganin cutar ga wanda bata tsananta ba ko take tsaka-tsakiya a cibiyar killacewa, muna kashe N100,000 a rana daya,” Abayomi yace.

Labarai Makamanta

Leave a Reply