Yaƙar CORONA: Ganduje Ya Zama Gwarzon Shekara

Wata kungiyar kwararru na Afirka mai suna African Professionals Renaissance Network, (APREN), da ke Dakar, Senegal ta zabi gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan da ya fi kwazo wurin yaki da COVID-19 a Najeriya.

A cikin wasikar da sakataren kungiyar Diouf Bakri Koalack, ya aike wa gwamnan, ya jinjina masa bisa jajircewarsa wurin yaki da annobar da ya karade duniya kamar yadda TVC ta ruwaito.

Kungiyar ta jadada cewa jajircewa gwamnan ya fito fili har ta kai ga Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa ta Najeriya, NCDC, ta yaba da kokarin gwamnan domin kowa ya sani.

Bayan nazarin yadda yaki da korona ke tafiya a jihohin kasar, “…mun fahimci cewa jihar Kano ta fita zakka a wurin yaki da annobar. Hakan kuma ya faru ne saboda jajircewa da kwazon gwaman wurin yaki da annobar.”

“Tun kafin bullar cutar a jihar Kano, mun gano cewa jihar ta kasance cikin shirin ko ta kwana. Bayan samun mutum na farko mai cutar a jihar, Gwamna Abdullahi Ganduje bai yi kasa a gwiwa ba wurin daukan matakan da suka dace.”

“Jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Ganduje ta yi gaggarumin aiki wurin dakile annobar COVID 19,” a cewar kungiyar.

APREN a matsayin ta na kungiyar kwararru daga kasashen Afirka ta haska fitilar ta zuwa wasu zababun kasashen Afirka kuma ta yi nazarin yadda jihohi suka dauki matakai a kan annobar.

A cewarsu, Kano ta zama abin misali ga sauran jihohi wurin yaki da COVID 19, inda ta kara da cewa, “A lokacin da jihar ta samu bullar cutar na farko, ta mayar da hankali sosai don karya lagwan ta.”

Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin yaki da annobar cikin gaggawa wacce ke dauke da kwararru da suka fahimci matsalar. Cikinsu akwai kwararru a fanin kiwon lafiya da sauransu.”

“Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Ganduje ta taka rawar gani wurin yaki da COVID 19 fiye da kowacce jiha a Najeriya. Kano ta zama cibiyar horas da maaikatan lafiya da wadanda ba na lafiya ba a arewacin Najeriya. Hakan ya yi wu ne domin kwazon gwamnan,” a cewar APREN.

Labarai Makamanta

Leave a Reply