Yaƙar CORONA: Bankin Duniya Zai Ba Najeriya Dala Miliyan 114

Bankin Duniya ya amince da shirin baiwa Nijeriya dala milyan 114 domin taimaka mata yaki da annobar corona virus wadda ta addabi kasashen duniya yanzu haka.

Bankin ya bayyana cewar dala milyan 100 daga cikin kudin rance ne, yayin da dala milyan 14 kuma tallafi ne da za’a rabawa jihohin kasar 36 da kuma gwamnatin tarayya domin sayen magunguna da kayan gwaji da kuma kayayyakin aikin likita.

Nijeriya na daya daga cikin kasashen da cutar tafi illa a nahiyar Afirka, inda ta kama mutane sama da 45,000 ta kuma kashe 930, yayin da kasar ke fuskantar matsalar yin gwaji.

Daraktan Bankin a Nijeriya, Shubham Chaudhuri ya ce Nijeriya na kokarin yaki da cutar amma kuma ana bukatar karin gwaji a matakan jihohi wadanda ke fuskantar matsaloli.

Labarai Makamanta

Leave a Reply