Bashir El-Rufai, ?an gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce Wallahi ya gwammace a datse masa kai a maimakon ya nemi afuwa’ game da hotonsa da amaryarsa Halima Nwakaego Kazaure.
Tunda farko da an yi ta sukar Bashir saboda hotunansa da matar da zai aura da ya wallafa a Twitter.
‘Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada ha?uri inji Bashir.
A hoto na farko da ya wallafa a ranar Talata – an gano shi ya ?ora hannunsa a ?ugun Halima yayin da a hoton na biyu kuma suna rungume da juna yana sumbatar kumatunta.
Sai dai wadanan hotunan basu yi wa wasu mutane da?i ba musamman wasu musulmi da ke ganin abinda da ya aikata haramun ne.
Da ya ke martani game da caccakar da wasu ke masa a ranar Laraba, Bashir ya ce masu sukar su fa?a masa idan akwai wani abu da zai iya yi don ya ?ara musu haushi.
“‘Idan hoto na da matata bai yi wa wasu dadi ba saboda shawararin da ban nema ba, ina son amfani da wannan damar in ce tabbas sakarkaru ne,”.
‘Idan akwai wata hanya da zan iya ?ara ?ata musu rai, don Allah a sanar da ni. Wasu har yanzu ba su fahimci cewa ba kowa ne sukarsu ke tada wa hankali ba.
Bayan wannan wani mai amfani da Twitter ya masa tambaya ya ce, ‘Ina fatar ba za su saka neman afuwa ba don abinda ka fa?i.’
“Na gwammace a datse min kai a maimakon inyi hakan. Allah ya kyauta. Shashasha da ba za su iya fitowa su nuna kansu ba”, Bashir ya bada amsa cikin gaggawa.