Watsi Da Mazhaba Ne Silar Fitina Tsakanin Musulmi – Sheikh Khalifa

An bayyana cewar watsi da tafarkin magabata na farko wato Mazhabobi da Malaman Musulunci suka yi ne, ya zama babbar hanyar da ta buɗe kofa ake samun miyagun maganganu da ake danganta su da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da wasu muggan Malamai ke yi.

Sanannen Malamin Addinin Musulunci mazaunin Birnin Zauzau Sheikh Muhammad Sani Khalifa ya bayyana hakan, a yayin gabatar da Hudubar Juma’a a masallacin kofar Fadar mai Martaba Sarkin Zazzau.

Shehin Malamin ya tabbatar da cewar riko da mazhaba shine hanya mafita akan dukkanin wasu matsaloli da suke damun al’ummar Musulmi, yayin da rabuwa da mazhaba ke jefa jama’a cikin ruɗani.

“A lokacin da malamai gaba daya suke kan mazhaba a Najeriya, ba’a samu wata fitina ba, amma yanzu da malamai suka watsar da mazhaba kowa ya koma kokarin kirkirar tasa fahimtar da mazhabar aka shiga rudani”.

“Yau kaji wancan malamin ya tsokalo wannan rigimar gobe kaji wancan ya tsokalo tashi rigimar abin har ya kai ga cin mutuncin Manzon Allah saw da iyalansa da sahabbansa Allah ya yarda da su”.

Wannan shine dalilin da yasa ya zama wajibi ga al’ummar musulmi matukar suna son zaman lafiya su riqi mazhaba, idan ba haka ba, ba za su fita daga cikin faganniya ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply