Watannin Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Afuwar Iyaye Da Daliban Jami’a

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin Tarayyar ta nemi afuwar ?alibai da iyayensu game da yajin aikin da ?ungiyar malaman jami’a ta ASUU ta yi na wata takwas.

Cikin wata sanarwa, Ministan ?wadago Chris Ngige ya tabbatar wa ?aliban cewa “ba za ku sake fuskantar irin wannan matsanancin yanayin ba a nan gaba”.

?ungiyar ta Academic Staff Union of Universities (ASUU) ta tsunduma yajin aiki ne tun ranar 14 ga watan Fabarairun 2022 saboda neman a inganta rayuwar malaman. Ta janye yajin ne a ranar Alhamis sakamakon wani hukuncin kotu da ya umarce su su koma.

“Tun da ASUU ta yarda ta bi umarnin kotu na janye yajin aikin, muna neman afuwar ?alibai da iyaye, wanda shi ma minista ?aya ne daga cikinsu, kan wannan lamari da bai kamata ba tun farko,” a cewar sanarwar da Olajide Oshundun ya fitar a madadin Mista Ngige.

Related posts

Leave a Comment