Rahotanni daga Kasar Saudiyya na bayyana cewar Yariman Saudiyya masoyin ‘kwallon kafa da kudi’, Yarima Abdullah bin Mosaad yana dab da mallakar kungiyar kwallon kasar Faransa ta Chateauroux.
Yariman wanda ya mallaki kungiyoyin wasanni na Sheffield United, Beerschot a Belgium, Kerala United a Indiya da Al Hilal United a UAE yana daf da kara sabuwar kungiya kan wadanda ya ke da su a baya.
“Mun dade muna sha’awar ?ungiyar kwallon kafa Chateauroux, mun yi nisa da tattaunawa batun sayen ?ungiyar” Yarima Abdullahi ya shaidawa AFP cikin hirar Zoom. “Kungiyar na cikin mayucin hali a mataki na biyu amma ina sa ran za ta farfado a nan gaba.”
A halin yanzu Chateauroux tana gasar kwallon kafa na Faransa inda ta samu nasarori hudu cikin wasanni 28 da ta buga.
Akwai yiwuwar za ta iya fadawa mataki na uku. Yariman, wanda ya taba jagorancin bangaren wasanni a gwamnatin Saudiyya ya bada umurnin a siya masa kungiyar ta Chateauroux don hada ta cikin jerin kungiyoyin da ya mallaka.
“Ina kaunar wasanni da kudi,” in ji Yariman mai shekaru 56 da aka kiyasta arzikinsa yakai Dala Miyan $240,000.
“A lokacin da na saka hannun jari a Ingila da Belgium, na yi farin ciki. Amma Faransa daban ne saboda kasar na tuna min kuruciya ta.
“Akwai ababe da yawa da na ke tunawa a kasar da dan uwa na (yarima) Abdulrahman a can aka haife shi. “Na san Chateauroux babu nisa daga Paris (kimanin kilomita 270) wani dalilin da zai sa in yi farin ciki idan na tafi Faransa bayan zuwa wurin cin abinci, shan shayi da wurin mike kafa.”