Al Sadd ta bada sanarwar cewa Xavi Hernandez ya tashi a ranar Juma’a, 5 ga watan Nuwamba, 2021. Jaridar AS ta fitar da wannan rahoton. Hakan ya kara tabbatar da rade-radin cewa Xavi Hernandez zai koma kungiyar Barcelona.
Hakan na zuwa ne bayan an kori Ronald Koeman daga aikinsa. Kungiyar Al Sadd tace Barcelona ta biya fam miliyan €5 domin ta dauke mai horas da ‘yan wasan.
AS tace Al Sadd ta fitar da jawabi tace Xavi ya amince ya koma Barcelona bayan biyan kudin da ke kansa, kamar yadda aka yi yarjejeniya a kwantiraginsa.
Kocin mai shekara 41 ya shafe shekara shida yana horas da kungiyar ta kasar Qatar. Watakila nan ‘yan awanni a bada sanarwar zuwansa a filin Camp Nou.
Kawo yanzu dai babu sanarwar da ta fito daga Barcelona a game da nada tsohon ‘dan wasan tsakiyan a matsayin babban mai horas da ‘yan kwallonta.
Da aka tambayi kocin da aka nada na wucin gadi kafin wasan Celta, ya sake jaddada cewa har yanzu ba a kai ga nada sabon mai horas da ‘yan wasa ba. Goal.com ta kawo rahoto cewa tsohon ‘dan wasan na kasar Sifen zai karbi aikin horas da kungiyar Barcelona daga hannun kocin rikon kwarya Barjuan.
Amma Sergi Barjuan ne zai jagoranci kungiyar ta Sifen a wasan Celta Vigo. Ana sa ran Xavi zai karbi ragamar kungiyar a wasansu na mai zafi da Espanyol. Al-Sadd ta wallafa bidiyo inda aka ga Xavi yana hawaye yayin da yake kukan ban-kwana da kungiyar. ‘Yan wasansa sun yi masa fatan alheri a kasar Sifen.