Ministan wasanni na Italiya, Mista Vincenzo Spadafora, ya yi magana a ranar Alhamis game da dawowar Ronaldo daga kasar Portugal.
Inda ya bayyana cewar ɗan wasan ya saba doka, domin babu rahoto daga hukumomin lafiya da suka ba da izini ga ɗan wasan na yin tafiye-tafiye.
Ronaldo ya na cikin ‘yan wasan da su ka fi kudi a Duniya ‘Dan wasan mai shekaru 35 ya ɗauko jirgin sama ya shigo Arewacin Italiya bayan an tabbattar da cewa ya na dauke da kwayar COVID-19.
Ana zargin ‘dan wasan da saba doka ganin yadda wasu ma’aikatan kungiyar kwallon kafan Juventus su ka kamu da Coronavirus a makon nan.
Amma kungiyar Juventus ta ce: “Cristiano Ronaldo ya dawo Italiya ne a jirgi bayan hukumomin lafiya sun tabbatar ‘dan wasan zai killace kansa.”
Ministan wasanni, Spadafora ya ce har yanzu dokar gwamnati ta na aiki, kuma har ga ‘yan kwallo. Yanzu haka duka ‘yan wasan Juventus su na killace, a dalilin kamuwa da cutar da Ronaldo da kuma ‘dan wasa Weston McKennie su ka yi.
A farkon makon nan ne aka yi gwaji inda aka tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar Coronavirus lokacin da ya ke wasa a gida. Hukumar kwallon kafa ta kasar Portugal ta sanar da haka a jawabi da ta fitar.