Wasanni: Ronaldo Da Messi Ba Su Samu Shiga Sahun Gwarazan 2020 Ba

Hukumar kwallon kafa ta Turai watau UEFA ta fitar da sunayen ‘yan wasa uku na karshe wadanda a cikinsu za a fitar da gwarzon shekarar 2019/20.

A wannan shekara babu sunan ko daya daga cikin manyan ‘yan wasan Duniya da su ka saba fice a ko yaushe, Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.

‘Dan wasan gaban Real ya huro wuta sai ya tashi daga kulob 1.
Kevin De Bruyne (Manchester City) ‘Dan wasan tsakiyan Manchester City ya yi abin a yaba a kakar bara bayan da ya yi sanadiyyar bada kwallaye 20, sannan kuma ya jefa kwallaye 13 da kansa a raga a gasar Firimiya.

 1. Robert Lewandowski (Bayern) Robert Lewandoski mai bugawa gaban Bayern Munchen shi ne ‘dan wasa na biyu a jerin. ‘Dan wasan na kasar Poland ya ci kwallaye 55, sannan ya lashe gasar gida da kuma na Nahiya.
 2. Manuel Neuer Bajintar Manuel Neuer mai tsaron gidan Bayern Munich ta sake fito da shi a shekarar bana.
  ‘Dan wasan da ke tsaron raga ya shafe wasanni shida ba tare da an zura masa kwallo a Turai ba.

‘Yan wasan kwallon kafa da su ka fi yawan kwallayen kasa Neuer, Lewandoski da De Bruyne.
Ragowar ‘yan wasan da su ke cikin sahun goma na farko su ne:

 1. Lionel Messi (Barcelona)
 2. Neymar Jr. (Paris Saint-Germain)
 3. Thomas Müller (Bayern)
 4. Kylian Mbappé (Paris Saint-Germain)
 5. Thiago Alcántara (Bayern)
 6. Joshua Kimmich (Bayern)
 7. Cristiano Ronaldo (Juventus)

Kungiyoyin Bayern da PSG ne su ka fi kowa tarin wakilai a shekarar nan. Kungiyoyin biyu su na da ‘yan wasa bakwai.
Barcelona, Juventus da Manchester City duk su na da guda.

A makon da ya gabata kun ji cewa Liverpool ta saye ‘Dan wasan tsakiyan kasar Sifen, Thiago Alcántara daga Bayern Munich baya ya lashe gasar cin kofin Nahiyar Turai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply