Wasanni: Mikel Obi Ya Yi Ritaya Daga Kwallon Kafa

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa na Najeriya Mikel John Obi ya sanar da ritayarsa daga wasan kwallon kafa.

Mikel Obi ya sanar da matakin ne ranar Talata a shafinsa na Instagram.

Ya lashe gasar Zakarun Turai a 2012 tare da tsohuwar kungiyarsa ta Chelsea, baya ga wasu jerin kofunan da ya lashe, kuma a baya-bayan nan yana buga wa kungiyar Kuwait SC ne.

Ga wani abu cikin sakon da ya wallafa a Instagram:

“Akwai wani karin magana da ke cewa komai na da karshe kuma haka lamarin yake ga wasan kwallon da na dade ina bugawa. Yau ita ce ranar da wasan kwallo ya zo karshe a rayuwata”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply