Wasanni: Messi Ya Ƙauracewa Atisaye Da Bercerlona

Lionel Messi ya kauracewa atasayen farko da Barcelona ta gudanar a jiya Litinin, domin sharar fagen shiga sabuwar kakar wasa.

Wannan na nufin mai yiwuwa kaftin din ya tilasta rabuwa da kungiyar Barcelona, ta hanyar kin bugawa kungiyar tasa wasa a sabuwar kakar wasan dake tafe, da za a soma ranar 12 ga watan Satumba.

Sai dai Messi da lauyoyinsa na ganin Shiga atasayen zai haifar da rudani kan ikirarinsu na cewar tuni Messi ya Raba Gari da kungiyar ta Barcelona.

Lauyoyin Messi sun kara da cewar Dan wasan na da damar amfani da Sashin dokar da ya bashi zabin komawa wata kungiyar a duk karshen kakar wasa, sai Barcelona ta dage kan cewar tun cikin watan Yuli wannan damar ta kufcewa Lionel Messi.

A ranar lahadi ne kuma hukumar shirya gasar LA- Liga ta Spain ta goyi bayan Barcelona kan sharadin muddin Messi na son rabuwa da kungiyar, Dole ya biya euro miliyan 700.

Gobe laraba mahaifin Messi kuma dillalinsa Jorge, zai gana da shugabannin Barcelona kan Makomar dansa.

Kungiyoyin Manchester City, PSG, Inter Milan, da Juventus ne ke kan gaba wajen kokarin kulla yarjejeniya da Messi da zaran ya rabu da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

Labarai Makamanta

Leave a Reply