Wasanni: El Rufa’i Ya Shiga Gasar Gudun Fanfalaki

Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna ya ce ya yi rajista domin shiga gasar tseren fanfalaki na kasa da kasa a jihar amma ba zai yi fiye da kilo mita biyar ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a ranar Asabar a Kaduna inda ya ce gasar da za ayi a ranar 21 ga watan Nuwamba zai ci kimanin Naira miliyan 300 kuma ana sa ran manyan ‘yan tseren duniya 10 za su shiga gasar.

A cewarsa, an shirya gasar ne domin gano matasa masu hazaka, da bawa matasa abin yi da kuma janyo hankulan masu saka hannun jari zuwa jihar.

Za ayi tseren ne na kilomita 21. Ya ce za a lashe kyautukan kudi kamar haka; Na farko a rukunin tseren manya zai samu $10,000 yayin da na goma kuma zai samu $1,000. A rukunin ‘yan Najeriya maza da mata kuma na farko zai lashe Naira miliyan 3 sannan na goma zai samu Naira 250,000.

“Wadanda suka shirya gasar ne za su dauki nauyin wadanda suka yi rajista. An shirya gasar ne domin kowa da kowa shi yasa aka saka shi mile 13 kawai ba kamar cikakken gudun fanfalaki na kwararru ba.
Masu gudun suna iya dakatawa a duk lokacin da suke so akwai 5km, 10. Ni kai na na yi rajista amma ba zan yi fiye da 5km ba.”

Gwamnan ya kara da cewa za a kara adadin kudin da wadanda suka lashe gasar za su samu idan za ayi na shekarar 2021. Ya kuma ce za a cigaba da yi kowanne shekara har zuwa 2023 a lokacin da wa’adin mulkinsa zai kare.

Ya cigaba da cewa motsa jiki sana’a ce kuma tana kara lafiya gashi hanya ce ta janyo hankalin matasa su zama kwararrun ‘yan wasanni na kasa da ma duniya.

Labarai Makamanta