Wasanni: Dalilin Barina ?ungiyar Kwallon ?afa Ta Saudiyya – Ahmed Musa

Fitaccen dan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Ahmed Musa mai shekaru 28 yana da dukiyar da ta kai $20 miliyan wanda ya samesu ta hanyar wasan kwallon kafa da tallace-tallace.

A yayin bayani a kan yadda babu zato balle tsammani ya bar kungiyar Al Nasssr da ke Saudi duk da tarihi mai kyau da ya kafa, Musa ya ce yana son komawa manyan gasa ne a Turai.

“Da kaina na bukaci na bar kungiyar kwallon kafan ta Riyadh duk da kuwa shekaru biyu na kwashe daga cikin kwagilar shekaru hudu da nasa hannu.

Ahmed Musa ya sanar da ESPN cewa da kanshi ya mika bukatar barin kungiyar kuma yayi sa’a suka amince.

“Na samu ganawa da kungiyar inda nace ina son datse kwangilata kuma suka yadda,” ya sanar da ESPN.

Ahmed Musa, daya daga cikin ‘yan kwallon kafa da aka fi biya a kasar Saudi Arabia, ya ce ya kasance mai burin komawa Turai.

“Na ji dadin zaman shekaru biyu da nayi a can kuma kungiyar kwallon kafan ta kyautata min,” Musa ya sanar da ESPN.

“Amma kuma ina son komawa Turai kuma ina tunanin wannan ne lokacin da ya dace in yi hakan.

“Ina son gogayya da manyan ‘yan wasan duniya. Ina mika godiyata ga kungiyar Al Nassr da kuma masoyana kan fahimtata da kuma fatan alheri da suke min.
Ba zan manta da su ba.”

Related posts

Leave a Comment