Wasanni: Croatia Ta Doke Morocco A Yunkurin Samun Matsayi Na Uku

Rahotannin dake shigo mana daga ƙasar Kasar Qatar na bayyana cewar Croatia ta taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da ake fafatawa a Qatar inda ta hau matakin na uku bayan ta doke Maroko da ci biyu da daya.

Wannan ne karo na uku da Croatia ke samu kyauta a gasar cin kofin duniya saboda a shekarar 1998 ita ce ta yi ta uku, sai kuma a 2018 ta zama ta biyu a gasar bayan Faransa ta doke taa wasan karshe.

A yau Lahadi ne za a buga wasan ƙarshe tsakanin kasar Faransa da Argentina.

Labarai Makamanta

Leave a Reply