An tabbatar da cewa ‘Dan wasan kungiyar kwallon AC Milan Zlatan Ibrahimovich ya na dauke da kwayar cutar murar COVID-19.
AC Milan ta bayyana cewa ta sanar da hukumar da ke da alhaki game da halin da ‘dan wasan kwallon kafan ya ke ciki a yanzu.
Kamar yadda kungiyar ta Seria A ta sanar a jiya, Zlatan Ibrahimovich mai shekaru 39 a Duniya zai fara killace kansa a cikin gida.
Wannan sanarwa ta fito ne a daidai lokacin da ‘yan wasan AC Milan su ke shirin buga wasan sharer fage zuwa karamin gasan Turai.
Milan za ta fuskanci kungiyar Bodo/Glimt na kasar Norwegiya, idan har ta yi nasara za ta samu zuwa gasar Europa League na 2020.
Shi ma ‘dan wasan gaban na kasar Siwidin, ya tabbatar da wannan lamari, ya ce ya kamu da wannan cuta ta numfashin mashako.
Zlatan Ibrahimovich ya sanar da hakan ne a shafinsa na Tuwita, ya ce amma har ya zuwa ranar Alhamis, babu alamun wannan cuta a jikinsa.
“A ranar (Laraba) gwaji ya nuna ba na dauke da kwayar cutar COVID-19, sai kuma a washegari Alhamis aka ce na kamu.” Inji Zlatan Ibrahimovich a Tuwita.
‘Dan wasan ya ce: “Babu wata alamar komai ko makamancin haka. Har COVID-19 ta yi karfin da za ta kalubalance ni. Ba ta yi dabara ba.”