Wasanni: Burina In Taka Leda A Amurka – Messi

Ɗan wasan Barcelona, Lionel Messi, ya ce yana da burin wata rana ya taka leda a Amurka, amma ya ce bai da tabbacin abin da zai faru nan gaba idan kwantiraginsa ta ƙare a watan Yuni.

Ɗan ƙasar Argentinar mai shekara 33, zai iya fara ciniki da kulob-kulob na ƙasashen ƙetare a watan Janairu.

Ce-ce-ku-ce kan makomar Messi a nan gaba ya ƙaru matuƙa tun bayan da Messi ɗin ya nemi barin kulob ɗinsa a watan Agusta.

“Ban san me zan yi ba tukuna,” haka Messi ɗin ya shaida wa tashar talabijin ta La Sexta ta Sifaniya.

“Zan jira sai ƙarshen kaka. Ina so na taka leda a Amurka domin sanin ya rayuwa take a can da kuma sanin yadda League yake a can, amma kuma zan dawo Barcelona da sauran ƙarfi na.

“A yanzu, abu mafi muhimmanci shi ne na mayar da hankali kan kulob ɗina na kammala wannan kakar da kyau, da kuma mayar da hankali wurin cin kofuna kada wani abu ya ɗauke min hankali”.

Barcelona, wadda ba ta ci kofi a kakar da ta gabata ba, ita ce ta biyar a La Liga bayan sun yi wasa mafi muni a farkon gasar cikin shekara 33.

Tun bayan da Messi ya shiga Barcelona lokacin yana da shekara 13, Messi ya zama wanda ya fi zama zakara a tarihin kulob ɗin ta ɓangaren cin ƙwallaye, inda ya ci La Liga 10, da kuma gasar Champions League sau huɗu da kuma lambar yabo ta Ballon d’Or sau shida – wadda lambar yabo ce da ake ba ɗan wasan ƙwallon ƙafa da ya fi shahara a duniya duk shekara.

Yunƙurin da ya yi a kwanakin baya na barin Barcelona ya ci karo da ra’ayin shugaban kulob ɗin, Josep Maria Bartomeu, wanda ya sauka a watan Oktoba.

“Wannan wani yanayi ne mai wuya ga kulob ɗin, amma waɗanda ke cikin kulob ɗin sun san yana cikin mawuyacin hali, abubuwa sun lalace kuma yana da wahala kulob ɗin ya koma yadda yake a baya,” a cewarsa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply