Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Arsenal ta lallasa Liverpool kwallo 5 zuwa 4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan yin kunnen doki na tsawon mintuna 90 a wasan da aka buga a filin kwallo Wembely.
Tsohon zakaran ‘yan kwallon nahiyar Afrika, Pierre-Emerick Aubameyang, ya fara zura kwallo ragar Liverpool a minti na 12. Sai da aka kusa tashi wasa Takumi Minamino na kungiyar Liverpool ya mayar da martani da kwallo a minti na 73.
A haka aka cigaba da karawa babu wanda ya kara zura kwallo cikin kungiyoyin biyu har minti 90 ya kare.
Yayinda aka shiga bugun daga kai sai mai tsaron gida ‘yan kwallon Arsenal sun daki raga a dukkan biyar da suka buga, hakazalika Liverpool illa Riham Brewster wanda ya tashi tsuntsaye maimakon dukan zare.
Ana buga wasan Community Shield ne tsakanin wadanda suka lashe kofin Firimiya da wadanda suka lashe FA.
Arsenal ta doke Chelsea ne a wasan karshe Firimiya yayinda Liverpool tayiwa Kora zarra ta lashe kofin Firimiya.