Wasanni: Ali Nuhu Ya Zama Jakadan La Liga

Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Hausa, furodusa kuma mai bada umarni, Ali Nuhu, ya bayyana a matsayin jakadan La Liga na arewacin Najeriya.

An bayyana jarumin a wannan matsayin a yayin taron farko na masoya La Liga na arewa wanda gidan rediyon Arewa da La Liga suka dauka nauyi a Kano.

Ali Nuhu ya tabbatar wa da masoyan La Liga na yankin arewacin Najeriya da cewa zai samar da alaka mai karfi kuma mai cike da zaman lafiya a yayin da ya zama jakadan La Liga a arewa.

Hakazalika, shugaban fannin labaran wasanni na gidan rediyon Arewa, Sherif Abdallah, ya ce Kano ita ce gidan La Liga, ya kara da cewa, wannan taron na farko shine zai zamanto tushen dukkan ababen arzikin da za su shigo kasar nan da arewa.

“Mun kawo La Liga kusa da masoyanta, mun kaddamar da ita a kusa. Ba za mu yi kasa a guiwa ba wurin ci gaba da karfafa alakarta da masoyanta a Najeriya,” Abdallah yace.

A yayin jawabi a taron, jakadan La Liga na Najeriya, Mutiu Adepoju ya nuna jin dadinsa a kan yadda suka samu masoya a Kano da sauran sassan arewacin Najeriya.

Labarai Makamanta