Mesut Ozil ya wallafa a shafin sa na Istagram irin halin ƙunci da cin zarafi da ake yi wa musulmi a yankin Uighur na kasar Chana, da nuna takaici da damuwa dangane da watsi da sha’anin su da sauran ƙasashen musulmi suka yi.
“Haƙiƙa an keta hakkin musulmi a Chana, ab kokkone musu Kur’anai da rusa musu Masallatai da kisan malaman su da yi wa matan su da ‘ya’yan su fyade, da tursasa matan su su auri ‘yan Chana da ba musulmi ba, amma babban abin damuwa ba wata ƙasa da ta nuna damuwa ko suka a kan wannan cin zarafin da aka yi, harda kasashen musulmi lallai wannan abin baƙin ciki ne da Allah ba zai bari ba.
Tuni dai kungiyar Kwallon ƙafa ta Arsenal ta nesanta kanta daga kalaman ɗan wasan na ta, inda ta ce ba da yawun ta ya yi wannan magana ba.
Sai dai a Martanin da ya bayar Mesut Ozil ya yi Allah wadai da nesanta kai da Arsenal ta yi akan kalaman na shi, inda ya zargi kungiyar da ƙoƙarin sanya harkar siyasa a cikin harkokin ta.
” Haƙiƙa Arsenal ta na da magoya baya masu yawa daga cikin Musulmi, kuma tabbas addu’o’in su na tasiri ga tasirin kungiyar, saboda haka musulmi ba su cancanci a wulakanta su ba, inji shi.