Waje: Saudiyya Ta Amince Da Da Ayyukan Umarah

Hukumar gudanarwar kasar Saudiya ta sanar da cewa, za ta bi matakai, wajen janye dokar dakatar da yin Umrah a Saudi Arabia da ta sanya sakamakon barkewar annobar COVID-19.

Ministan aikin Hajj da Umrah, Mohammed Saleh Benten ya ce za su ci gaba da daukar lafiyar al’umma a kan komai, kuma ma’aikatarsa na duba matakai 3 na dawo da ibadar.

Shafin Haramain Sharifain a Twitter, ya sanar da cewa, matakin farko, za a amincewa mutane 6,000 yin ibada a kowacce rana, matakin zai fara daga ranar 4 ga watan Oktoba, 2020.

A mataki na biyu, za a amince mahajjata 15,000 su yi ibada a kowacce rana, da kuma masu yin Umrah 40,000 a kowacce rana, matakin zai fara daga ranar 18 ga watan Oktoba 2020. A mataki na uku, za a dawo da aikin Umrah ba tare da doka ba, mutane na iya zuwa daga kowacce kasa, akalla Mahajjata 20,000 da masu Umrah 60,000 a kowacce rana.

Za a fara mataki na uku daga ranar 1 ga watan Nuwamba 2020, a cewar ma’aikatar cikin gida ta aikin Hajji da Umrah.

A ya yin bin wadannan matakai, ma’aikatar ta ce za ta tabbatar da anbi matakan lafiya domin dakile barkewa ko yaduwar annobar COVID-19. Ma’aikatar ta kuma jaddada bukatar yin rejistar zuwa Umrah da wuri, tana mai cewa, hukumomi ko kamfanoni da ke jigilar masu ibadar su tabbatar da yin gwajin lafiya.

A halin yanzu, al’ummar kasashe 80 ne za su iya ziyartar kasar Saudiya domin yin Umrah ba tare da bukatar takarad Visa ba, kuma za a kara adadin, a cewar ma’aikatar.

A shekarar 2019, ‘yan asalin kasar Saudiya 5.3m ne suka yi aikin Umrah, sai mazauna kungiyar kasashen GCC mutum 1.2m, sai 7.5m daga sauran kasashe, da 6.4 daga ‘yan ci ranin Saudiya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply